Ibori ya koma Najeriya bayan zaman kaso a London

Nigeria Ibori

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A 2012 ne aka daure Mista Ibori a London

Tsohon gwamnan jihar Delta a Najeriya wanda hukumomi a Burtaniya suka daure a kurkuku bisa aikata laifin zarmiyar kudi da cin hanci, James Ibori ya koma Najeriya.

A cikin watan Disamban bara ne aka sako Mista Ibori daga gidan yari a London, bayan ya shafe shekaru hudu daga cikin shekaru goma sha uku da aka yanke mushi.

Dandazon magoya bayanshi ne suka taru a Osubi dake Warri don tarban tsohon gwamnan.

A shekarar 2012 ne aka daure Mista Ibori a London bisa aikata laifin zarmiyar kudi da ya kai dala miliyan saba'in da takwas da rabi, bayan ya yi ta zillewa kamu daga jami'an tsaro a Nageriya

A 2010 ya je Dubai, a inda daga nan ne aka tasa keyarshi zuwa Burtaniya.

Masu rajin yaki da cin hanci da rashawa sun ce a kowacce shekara, ana fita da biliyoyin fama-famai na haramtattun kudade daga Najeriya, inda ake bi ta Burtaniya da su ko kuma wasu kasashe dake karkashin ikon Burtaniya.

A saboda haka ne suka ga cewa daurin da aka yi wa James Ibori a London wata babbar nasara ce da ba a saba gani ba a yaki da cin hanci da rashawa a duniya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mista Ibori ya ce zai daukaka kara kan hukuncin da aka yanke mushi

Mista Ibori dai ya sha alwashin daukaka kara game da hukuncin da aka yanke mushi, inda ya ce akalla daya daga cikin jami'an 'yan sanda da suka gudanar da binciken ya karbi cin hanci.

Sai dai 'yan sandan birnin London sun ce sun binciki zargin da Mista Iborin ya yi kuma ba bu wata tuhuma da aka yi.

A ranar Juma'a, kungiyar yaki da cin hanci a duniya ta Transparency International ta ce ikirarin daukaka kara da Mista Ibori ya yi, cin fuska ne ga harkar shari'a.

Ra'ayi ya sha ban-ban a Najeriya akan ko yakamata a sake gurfanar da Mista Ibori a gaban kotu, yayin da ya koma kasar, ganin irin dukufa da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Wasu rahotanni sun ce duk da cewa ya na daure a kurkuku, Mista Ibori ya taka rawa a zaben gwamnan jihar Delta mai ci yanzu.