Chelsea ta yi tazarar maki 12 a gasar Premier

Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan wasan Chelsea

Chelsea ta kara fadada tazarar dake tsakaninta da da sauran kungiyoyin gasar Premier ta Ingila, bayan da ta lallasa Arsenal da ci 3-1 a karawar da suka yi ranar Asabar a Stamford Bridge.

Kocin Arsenal, Arsene Wenger wanda ya kalli wasan daga cikin 'yan kallo, ya yi fatan kulob din zai farfado daga kashin da ya sha a hannun Watford.

Doke Arsenal da Chelsea ta yi, ya sa yanzu ta shiga gaban Arsenal da maki goma sha biyu.

Marcos Alonso ne ya fara ci wa Chelsea kwallo a minti na 13 da fara wasa, sannan Eden Hazard ya zura ta biyu bayan minti takwas da dawowa daga hutun rabin lokaci.

Cesc Fabregas ya ci kwallo ta ukun bayan da mai tsaron ragar Arsenal Petr Cech ya kuskuren bashi kwallo a kafarsa.

Olivier Giroud ne ya ci wa Arsenal kwallo dayar ana gab da tashi wasa.

Tazarar maki 12 ne kuma ke tsakanin Chelsea da mai biye mata wato Tottenham.

Yanzu haka, Chelsea ce ke jan ragama a teburin gasar da maki 57, a inda ita kuma Arsenal take ta uku a teburin da maki 47.