Dusar kankara ta sanya mutane sun makale yankunan Afghanistan

Dusar da ta mamaye tsaunuka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kankarar ta mamaye manyan tituna, hakan kuma ya janyo cikas a harkokin sufuri

Dusar kankara mai tarin yawa da ta sauka a arewa maso gabashin kasar Afghanistan ta hallaka akalla mutane goma.

Jami'ai yankin na fargabar ta yi wu wasu mutanen sun makale a cikin kankarar, a yankin Badakhshan saboda yadda kankarar ke zuba a wurin.

Kankarar dai ta mamaye gidaje da tituna har ma da motocin da ke aje a kofar gidaje.

Haka kuma dusar kankara da ke zuwa a Sauran yankunan Afghanistan ciki kuwa har da gundumar Bamiyan da Balkhab da ke arewacin kasar sun sanya harkokin sufuri tsayawa cak.