Zanga-zangar lumana ta farar hula a Niger

Zanga-zangar kungiyoyin farar hula a Nijar
Kungiyoyin farar hula sun gudanar da zanga-zangar lumana, ta ci gaba da matsa wa gwamnatin kasar lamba, domin ta dauki mataki nagari wajen kyautata rayuwar al'uma baki daya.
A halin da ake ciki dai ,yanayin rayuwar jama'a talakawa da ke zaune a yankunan karkara da ma'aikatan gwamnati na dada tabarbarewa a kasar ta Nijar , kamar yadda kungiyoyin suka yi korafi.
Sun kara da cewa duk da hakan, gwamnatin kasar kuma ta nuna hali na ko in kula kan wannan lamari da jama'ar kasar ta Nijar da dama ke ciki.
Matsaloli da dama ne kungiyoyin suka aiyana.Kama daga matsalar ruwan sha da wutar lantarki da tsadar abinci da handama da suke zargin ana yi da rashin adalci a cikin kasa da dai sauren su.
Daga bangaren jam'iyar PNDS Tarayya mai mulkin kasar, na furta cewa ba gaskiya ba ne korafin da 'yan farar hular ke yi.
Bangaren dai na gwamnati na bayar da hujar cewa, hukumomin kasar ta Nijar na yi bakin kokarin su, domin kyautata al'amurra a fadin kasar baki daya.
Wannan zanga-zanga ta gudana ne bayan da bangaren gwamantin tuni ya gudanar da tashi zanga-zangar ta nuna goyon baya a makon da ya gabata.