Jesus ya taka wa Man City rawar gani

Gabriel bai dade da zuwa Man City ba
Bayanan hoto,

Gabriel Jesus ya ci wa Man City kwallaye biyu

Dan wasan Manchester City, Gabriel Jesus ya ci wa kungiyar kwallaye biyun da ta ci Swansea, a wasan da suka tashi 2-1, ranar Lahadi.

Yanzu haka dai Man City ce mai matsayi na uku a teburin gasar Premier da maki 49.

Sai dai kuma Swansea ta samu ta rama kwallo daya ta hannun dan wasanta, Gylfi Sigurdsson, bayan hutun rabin lokaci.

Swansea tana da maki 21 kuma na gab da sulmiyowa daga teburin daga gasar.