Celtic: Dembele ya ci kwallaye uku

Moussa Dembele
Bayanan hoto,

Moussa Dembele ya ci kwallaye uku

Dan wasan kungiyar Celtic, Moussa Dembele ya ci wa kungiyar tasa kwallaye uku, a wasan da ta taka da St Johnstone, ranar Lahadi.

Yanzu haka Celtic ce ja-gaba a teburin gasar Premier ta Scottland da maki 27.

Wannan ita ce nasarar da Celtic ta samu karo na 19 a jere.

Ita kuma St Johnstone ta kasance mai matsayi na biyar a teburin.