2Face ya fasa jagorantar zanga-zanga a Nigeria

2face

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

2Face ya ce ya soke zanga zangar ne saboda dalilai na tsaro

Fitaccen mawakin nan dan Najeriya, Innocent Idibia wanda aka fi sani da 2Face ya soke jagorantar wata babbar zanga-zanga da ya shirya yi a kasar ta nuna rashin jin dadi game da yadda gwamnati ke tafiyar da tattalin arzikin kasar.

A makon jiya ne mawakin na Afro-Pop, ya buka ci 'yan Najeriya da su fita zanga zangar a ranar Litinin shida ga watan Fabrairu saboda tabarbarewar tattalin arzki da kasar ke fuskanta, da tsadar kayan masarufi.

Yanzu 2Face ya ce ya soke jagorantar zanga-zangar, inda ya bayar da dalilai na tsaro.

A ranar Alhamis, rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi barazanar cewa ba za ta bari a gudanar da zanga-zangar ba, saboda bata gari sun yi shirin amfani da damar wajen tayar da fitina.

A wani sakon bidiyo da ya sanya a shafinsa na instagram, 2Face ya ce "ya ku 'yan Najeriya, bayan shawarori da muka nema, mun gano cewa zanga-zangarmu mai taken #OneVoice da muka so yi a Lagos da Abuja ranar Litinin 6 ga watan Fabrairu ta na fuskantar barazana daga wajen wasu wadanda ba aniyar mu daya ba. Abin da muke so mu cimma bai kai darajar ran dan Najeriya ba".

Asalin hoton, 2face

Bayanan hoto,

2Face ya ce zai sanar da magoya bayansa abin da ya cimma nan gaba

Ya ce manufar zanga zangar ita ce mu nemi a kyautata rayuwar 'yan Najeriya.

"A saboda haka, ina sanar da oke zanga-zangar. Za mu sanar da ku abinda muka cimma nan gaba".

Tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya ta kara muni ne tun bayan faduwar farashin mai a kasuwannin duniya, abin da ya jefa tattalin arzikin kasar cikin munnunan hali.

Lamarin ya kuma ci gaba da ta'azzara ne yayin da 'yan bindiga a yankin Niger Delta mai arzikin mai ke ci gaba da fasa bututan mai, da kuma manufofin gwamnatin kasar da suka shafi musayar kudaden waje.