Dusar kankara ta kashe mutane a Afghanistan da Pakistan

Asalin hoton, Reuters
Rufin gidaje da dama ya rufta saboda nauyin dusar kankarar
Dusar kankara dake sauka daga sama ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a kasashen Afghanistan da Pakistan.
Fiye da mutane dari daya ne dusar kankarar ta kashe a Afghanistan, da suka hada da wasu fiye sittin da tsaunukan kankara suka rufto ma wa a tsakiya da gabashin kasar.
A hanyar karkashin kasa ta Salang, wacce ta wuce zuwa tsaunukan Hindu Kush, gwamman direbobin motoci sun makale, kuma ba su da abinci ko tsabtar wurin zama.
Rahotanni sun ce wasu mutane biyu sun sandare saboda tsananin sanyi har suka kai ga mutuwa.
Dusar kankarar ta rufe wasu gidaje a Kabul, babban birnin kasar, sannan an rufe babban filin jirgin sama dake birnin.
A yankunan Himalayan a arewacin Pakistan, ruftawar tsaunukan kankara ta kashe akalla mutane goma.