Buhari ya tsawaita hutun da ya dauka

Shugaba Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A baya dai Shugaba Muhammadu Buhari ya ki cewa uffan kan batun rikicin na APC

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya daga ranar da zai dawo Najeriya daga hutun da yake yi a Ingila.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin, Femi Adesina, ya wallafa, a shafinsa na Facebook, ya ce, shugaban ya rubuta wa Majalisar Dokokin kasar takardar neman karin kwanaki.

Sanarwar ta ce shugaban ya nemi a tsawaita lokacin dawowar shugaban domin samun damar yin wasu gwaje-gwaje da likitoci suka umarce shi da yi.

Sai dai kuma sanarwar ba ta fayyace takamaimai ranar da shugaban zai dawo ba.

A ranar 6 ga watan Fabrairu 2017 ne dai ake sa ran dawowar shugaban daga hutun da ya dauka wanda ya fara ranar 19 ga watan Janairun 2017.

Shugaban dai yana hutun nasa ne a Ingila a inda kuma ake duba lafiyarsa.

Mataimakin shugaban, Farfesa Yemi Osinbajo ne dai mukaddashin shugaban har zuwa lokacin da zai dawo.

Ko me hakan ke nufi?

Usman Minjibir, Sharhi

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce babu wata karamar hukuma a kasar da ke hannun 'yan Boko Haram

Sanarwar dai wadda Femi Adesina ya fitar ta ce karin hutun yana da nasaba ne da karasa wasu gwaje-gwajen da likitoci suka umarce shi da ya yi.

To sai masu sharhi na kallon dagin da aka samu da irin halin rashin lafiyar da yake fama da ita.

A baya dai an ta cece-kuce kan rashin lafiyar shugaban, a inda har ta kai ga wasu suka fara zargin ko Buhari ya rasu ne.

To sai dai makusanta shugaban sun ta sanya hotunansa a kafafen sada zumunta tare da iyalensa da ma wasu manyan kasa kamar gwamnoni da dai sauransu.

Hakan kuwa ya janyo cacar-baka tsakanin 'yan kasar, a inda wasu ke karyata hotunan da cewa ba na yanzu ba ne.

Har wa yau dai, wani ba'arin 'yan Najeriyar na alakanta tsawaita hutun na shugaba Buhari da batun zanga-zangar da wani matashin mawaki da aka fi sani da 2Face ya nemi ya yi a ranar Litinin, ranar da ya kamata shugaban ya dawo ta asali.

Sai dai kuma a ranar Lahadi ne mawakin ya sanar da janye znga-zangar duk da cewa wasu kungiyoyi masu rajin kare hakkin Dimokradiyya sun ce ba gudu babu ja da baya.