Kun san cutar da ke damun Muhammadu Buhari?

Bayanan sauti

Kun san abin da ya hana Buhari komawa Nigeria?

Fadar shugaban Najeriya ta ce rashin lafiyar Shugaba Muhammadu Buhari wani sirri ne tsakaninsa da likitansa wanda bai kamata wani mutum ya sani ba.

Kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa Muhammadu Buhari bai koma kasar kamar yadda aka tsara ba ne saboda likitansa ya bukaci ya zauna domin sake duba lafiyarsa.

Ya kara da cewa, bayan an gudanar da gwaji a kan shugaban kasar sau daya, an sake yin gwaji a kansa kuma sakamakon gwajin na biyu ake jira shi ya sa likitan ya bukaci Shugaba Buhari ya zauna har sai an fitar da sakamakon.

Sai dai ya ce yana fatan ba za a dauki dogon lokaci ba kafin a fitar da sakamakon gwajin na biyu.

Da BBC ta tambaye shi kan ko wacce rashin lafiya ce ke damun shugaban kasar, sai Mista Shehu ya ce, "Wannan sirri ne tsakanin maras lafiya da likitansa".

Amma ya yi kira ga 'yan Najeriya su yi wa shugaban kasar addu'a.

A ranar 19 ga watan Janairun 2017 ne dai shugaban ya ce zai tafi hutunsa ranar 23 ga watan Janairu, sannan ya dawo ranar shida ga watan Fabrairu.

Amma a ranar biyar ga watan Fabrairun sai ya turo wa majalisar kasar neman kara masa wa'adin hutun.