Kusan mutum dubu 500 sun bi sahun zanga-zanga a Romania

Asalin hoton, AP
Ana zanga-zangar ne a kan dokar kankare laifi ga wasu nau'o'in cin hanci
An kiyasta cewa mutane kusan rabin miliyan sun bi sahun zanga-zangar da ake yi tsawon kwana shida a jere a Romania, duk da cewa gwamnati ta janye shirinta na kin hukunta mutanen da suka aikata wasu laifuka da suka shafi cin hanci.
Zanga-zangar ita ce mafi girma tun bayan faduwar gwamnatin gurguzu ta Nicolae Ceausescu a shekarar 1989.
Da yawa daga cikin masu zanga-zangar na dari-dari da matakin gwamnatin na soke dokar cin hancin wadda yanzu za a gabatarwa majalisar dokoki, inda wasu kuma ke san gwamnatin hadaka ta sauka.
Jagoran karamar jam'iyyar da ke cikin hadakar, Calin Tariceanu, ya shaidawa BBC cewa, ba a gudanar da sauye-sauyen yadda ya kamata.
Amma kuma ya ce sauye-sauye ne da aka bullo da su da kyakkyawar niyya wadanda za a aiwatar a bangaren shari'a na kasar da kuma hukumar leken asiri ta kasar.