Morocco ta ce ba za ta canja matsayinta a kan yammacin Sahara ba

Morocco ta fice ne daga tarayyar Afirka saboda takaddama a kan 'yancin yammacin Sahara
Bayanan hoto,

Morocco ta fice ne daga tarayyar Afirka saboda takaddama a kan 'yancin yammacin Sahara

Wani minista a Morocco ya ce kasarsa ba zat a ta ba amincewa da 'yancin yankin yammacin sahara ba, sannan kuma za suyi kokarin shawo kan gwamnatocin kungiyar tarayyar Afirka da su canja shawara kan amincewar da suka yi da yankin.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar, Nasser Bourita ya yi wannan bayani a wata hira da ya yi da wani shafin intanet na Morocco da ke amfani da harshen Faransanci mai suna Le Desk.

Ya dai yi wadannan kalamai ne kasa da mako guda da aka sake karbar kasar a kungiyar tarayyar Afirka, bayan ta fita a shekarar 1984 sakamakon rikici akan yankin.

Mr Bourita ya ce kasancewarsu a matsayin mamba a kungiyar tarayyar Afirka ba zai canja matsayinsu na cewa yankin yammacin sahara bangare ne na kasar Morocco ba.