Wata mata ta boye gawar jariranta shida a akwati

Winnipeg

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An samu gawawwakin e a kamfanin ajiya na Winnipeg

Ana tuhumar wata mata a birnin Winnipeg da ke Canada da laifin boye gawawwakin jariranta guda shida a cikin akwati (loka).

Kotu ta yankewa Andrea Giesbrecht hukuncin daurin shekara biyu kan ko wacce gawa daya da ta boye, wanda hakan ke nufin za ta yi zaman gidan yari na shekara 12.

A ranar Litinin ne alkalin kotun yankin Manitoba, Murray Thompson, ya yanke hukuncin bayan an kwashe tsawon wata daya ana gudanar da shari'ar.

An samu gawar jariran ne a cikin loka a watan Oktobar 2014.

Mai shari'a Thompson ya ce hujjojin da aka gabatar sun tabbatar da cewa Ms Giesbrecht, ta boye wa duniya daukar cikinta da kuma haihuwar jariran shida alokuta daban-daban.

Ma'aikatan da ke goge-goge a wani kamfanin ajiya na U-Haul ne suka kira hukumomi bayan sun gano gawawwakin jariran.

Bayanan hoto,

Mai shari'a Murray Thompson ya yanke wa matar hukuncin daurin shekara 12

An samu gawawwakin jariran sabuwar haihuwar ne a lokacin da suka fara rubewa. Ba tare da bata lokaci ba aka kama Ms Giesbrecht.

Masu bincike sun kasa gano musabbabin mutuwar jariran ko kuma tabbacin cewa a raye aka haife su ko a mace.

A hukuncin da ya yanke, mai shari'a Thompson ya ce, hujjar da likitoci suka gabatar ta nuna cewa, "kamar an haifi jariran ne a raye."

Sai dai ba a samu wata hujja da ke nuna cewa Ms Giesbrecht ta ga likita ba a dukkan lokutan da take dauke da ciki sau shida.

An samu kayan wasan yara kusa da gawawwakin jariran a cikin lokokin.

Alkalin ya ce, "Babu wata alama da ke nuna cewa ta fuskanci wata barazanar lafiya a lokacin da take da cikin, alamu sun nuna cewa ta san za ta haifi yaranta a raye shi yasa ta boye cikinsu da haihuwarsu," inji mai shari'ar.

Zuwa yanzu dai ba a saka ranar da za a kai ta gidan yari ba.