Nigeria: 'An kashe tirilyan uku a wutar lantarki a banza'

Har yanzu ba ta sauya zani ba game da lantarkin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Har yanzu ba ta sauya zani ba game da lantarkin Najeriya

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Yakubu Dogara, ya ce, kasar ta kashe Naira Tiriliyan 2.74 kan wutar lantarki daga 1999 zuwa 2015, amma har yanzu bata yi tasiri ba.

Mista Dogara wanda yake gabatar da jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki kan wutar lantarki, ya ce, a duk lokacin da aka fitar da makudan kudi don gyaran wuta, sakamakon da ake samu shi ne karin duhu.

Sai dai kuma Yakubu Dogara ya yi wasu tambayoyi da ya ce, amsarsu ita ce hanyar lalubo bakin zare kan samar da wutar lantarki a Najeriya.

Tambayoyin da Dogara ya yi sun hada:

 • Me ya sa fiye da shekara 56 wutar Najeriya ba ta wuce karfin Megawatz 5000 ba?
 • Mene ne dalilin da ya sa tsare-tsaren gwamnatocin baya suka kasa yin tasiri?
 • Me ya sa har yanzu kayayyakin rarraba wuta suka yi karanci?
 • Ta yaya ne gwamnatin tarayya za ta samar da wadatattun kayan rarraba wuta?
 • Mene ne dalilin da ya sa har yanzu babu wadatattun mitoci amma ake yanka wa mutane kudin da suka sha wuta?
 • Ta yaya ne Hukumar Sanya Ido kan Wutar Lantarki ta NERC za ta samar da harajin wutar da babu cuta babu cutarwa.
 • Me ya sa babu wani tsarin azo-a-gani wajen gina tashoshin wuta na iskar Gas?
 • Wane tsari ya kamata a yi wajen ganin an daina fasa bututun mai da na iskar Gas?
 • Wacce hanya ya kamata a bi wajen karfafa wa masu sanya hannun jari gwiwa kan samo da sarrafa da kuma rarraba iskar Gas.
 • Mene ne dalilin da ya sa masu sanya hannun jari ke shakkun sanya jari a fannin wutar lantarki?
 • Me ya sa bankunan gida da na waje ba sa son zuba kudade a harkar wutar lantarki?
 • Ta yaya za a yi amfani da kananan tafkuna da hasken rana wajen sama wa kauyuka wutar lantarki?
 • Bai kamata a ce gwamnati ta mayar da hankali kan amfani da kwayayen wuta marasa jan wutar da yawa ba?
 • Wacce rawa Majalisar Dokoki za ta iya takawa wajen samar da wutar lantarki a Najeriya?

A don haka kakakin majalisar ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su nemo amsar wadannan tambayoyi don da su ne za a samu mafita.

Matsalar rashin wutar lantarki dai ta yi kamari a Najeriya, wadda har yau ba a samu shawo kanta ba.

Hakan kuma yana durkusar da harkokin kasuwanci da dama da masana'antu, wadanda suke taka rawa wajen inganta tattalin arzikin kasar.