'Na sa mata fadawana bisa shawarar Turawan Canada'

Asalin hoton, Getty Images
Sarkin Banyo, Muhammad Gabdo Yahaya, ya sa mata sun zama fadawa, a fadarsa da ke Arewacin kasar Kamaru.
Sarkin dai ya ba su matsayi na musamman domin bayar da shawara kan matsalolin da suke ci wa mata tuwo a kwarya.
Sarki Gabdo ya ce, "Ambasadan Canada ya zo nan ya kwana uku, a inda ya shaida mana cewa suna son taimaka wa mata amma ba ta hannun mazajensu ko kuma gwamnati ba saboda tsoron yin fice."
"Saboda haka tallafin zai rinka biyowa ta hannun sarakan gargajiya. Wannan ne ya sa muka ba su matsayi na musamman a fadarmu." In ji Sarki Gabdo Yahaya.
Baya ga zaman fada, fadawan mata na wakiltar sarkin a wurare daban-daban.
An kafa masarautar Banyo a lardin Adamawa a shekara ta 1823, ita ce ta share fage wurin bude wa mata tara kofa masu rike da wasu mukamai da suke da alaka da kyautata rayuwar iyali.
Bisa ga al'ada maata a yankin Arewacin Kamaru ba sa jerawa da maza a wuri guda.
A baya can matsayin da wadannan mata suke da shi, shi ne na gudanar da ayyukan gida da kuma bi sau da kafa duk wasu matakan da aka dauka a kansu.