An haramta sanya kayan da ke matse jiki a Lagos

Wata daliba

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dalibai na yin shigar da ke nuna al'aurarsu

Jami'ar Lagos da ke Najeriya ta haramta wa maza da mata sanya tufafin da ke matse jiki, sannan ya fito da surar jikin nasu.

Wata sanarwa da jami'ar ta fitar, wadda kafofin watsa labaran kasar suka ambato, ta ce tufafin da aka hana sanya wa sun hada da matsattsun turoza da sket da bulawus.

Hukumomin jami'ar sun kuma haramta sanya "duk wasu tufafi da ke nuna tsaraicin mutum da suka hada da nuna kirji da ciki da ƙasan cinya da katara ko duwawu".

Sanarwar ta bukaci dalibai su "rika yin shiga ta kamala a cikin jami'a. Sanya tufafin da ke matse jiki da rigunan da ba su da madaurin kafada da kuma wadanda ke nuna al'aura ba su dace ba."