Pakistan ta haramta fim ɗin Shah Rukh Khan

Shah Rukh Khan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fim ɗin Raees ya yi kasuwa a lokacin da aka fitar da shi kasuwa

Hukumomin Pakistan sun haramta fitar da wani sabon fim mai suna Raees na fitaccen tauraron Indiya, Shah Rukh Khan.

An ranar 2 ga watan Fabrairu aka tsara fitar da fim ɗin a Pakistan wanda kuma ya ƙunshi jarumi Mahira Khan ɗan ƙasar Pakistan.

Babbar hukumar tantance fina-finai ta Pakistan ba ta bayar da wani bayani a hukumance kan dalilin hana fitar da fim ɗin ba.

Sai dai, wani jami'in hukumar ya fada wa BBC Urdu cewa dalili guda shi ne fim ɗin ya "nuna musulmi a matsayin masu aikata laifi kuma 'yan ta'adda".

Da aka saki fim ɗin a watan Disamba, musulmi 'yan Shia sun yi fatali da wasu sassa a cikinsa, musammam inda ake nuna jerin gwanonsu na shekara-shekara.

Labarin fim ɗin Raees ya ta'allaƙa ne a kan wani tauraro mai suna Raees Alam, wani jagoran mafia kuma musulmi wanda ya shimfiɗa wata ƙasaitacciyar daular barasa a cikin jihar Gujarat a kudancin Indiya, inda aka hana sha da sayar da giya.

Wani jami'in kamfanin da ke cinikin fim ɗin, ya faɗa wa BBC cewa hukumar tace fina-finan ta yi nazarinta a ranar Juma'a, kuma a ranar Litinin ta ce ta haramta sayar da shi.

Wani mai harkar fina-finai Nadim Mandviwala ya ce Raees "gawurtaccen fim ne" kuma haramcin da hukumomi suka yi masa "ba alheri ba ne ga kasuwanci, amma idan gwamnati na jin fim ɗin ka iya tayar da zaune tsaye, to mai yiwuwa shawarar ta dace".

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Jaruman Indiya da Pakistan suna haɗin gwiwa cikin harkokinsu na yin fim

Sai dai, wani daraktan fim a Pakistan, Jami Mehmood ya soki wannan shawara.

"kamata ya yi mutane su riƙa haƙuri da ra'ayoyin wasu. Kamata ya yi mu riƙa kallon fina-finan Indiya da tunanin mutanen Indiya, kamar yadda ake kallon fina-finan Iran a Amurka."

Pakistan ta ƙaƙaba wani haramci na rabi-da-rabi kan fina-finan Indiya tun bayan yaƙin 1965 tsakanin ƙasashen biyu, kuma bayan yaƙin Bangladesh a 1971, sai ta haramta su kwata-kwata.

Matakin a hankali ya janyo durƙushewar harkar fina-finai a Pakistan, kuma ya nakasa al'adar zuwa silima da ta taɓa yin tashe.

Sai dai a shekara ta 2007, Pakistan ta ɗage haramcin. Fina-finan Indiya sun matuƙar fice a Pakistan, har ma ana alaƙanta su da taimaka wa bunƙasar silimomi masu majigi da yawa a manyan biranen ƙasar.

A watan Satumbar bara, ƙungiyar masu shirya fina-finai ta Pakistan ta haramta tantance fina-finan Indiya, bayan takwararta ta Indiya ta hana sanya jaruman Pakistan a fina-fina ƙAsar.

Matakin ya zo ne bayan wani harin 'yan tada-ƙayar-baya da aka kai kan wani sansanin sojin Indiya a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Indiya, harin da Indiya ta zargi 'yan tada-ƙayar-baya daga Pakistan da kai wa.