Ko hana musulmi shiga Amurka, wariya ce?

US Protester

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mutane da dama a Amurka na nuna adawa da matakin hana musulmi shiga Amurka

Kotun ɗaukaka ƙara a Amurka ta tambaya ko matakin shugaba Donald Trump na hana musulmi shiga ƙasar, ya nuna musu wariya.

Umarnin shugaban ƙasa ya haramta wa dukkan 'yan gudun hijira da baƙi shiga Amurka na wucin gadi daga akasari ƙasashen musulmi bakwai, kafin a dakatar da shi a cikin makon jiya.

Mai shari'ah Richard Clifton ya tambaya ko hakan ka iya zama wariya idan ya shafi kashi 15 cikin 100 na musulmin duniya.

Yana ɗaya daga cikin alƙalan kotun ƙoli guda uku a San Francisco, da za ta yanke hukunci nan gaba cikin wannan mako.

Ɓangaren biyu sun shafe tsawon sa'a guda a ranar Talata suna tafka muhawara ga-da-ga.

Kowanne irin hukunci kotun ɗaukaka ƙara mai mataki na 9 za ta yanke, mai yiwuwa ƙarar za ta dangana har kotun ƙoli.

Me ɓangaren biyu ke cewa a gaban kotun ɗaukaka ƙara?

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ma'aikatar shari'ah ita ce farko ta fara gabatar da bahasi, inda ta buƙaci alƙalan ɗaukaka ƙarar sun sake tabbatar da umarnin haramcin.

Lauya August Flentje ya ce majalisar dokokin Amurka ta bai wa shugaban ƙasa iko na iyakance waɗanda za su iya shiga ƙasar.

Da aka tambaye shi ya bayar da shaidar cewa ƙasashen da abin ya shafa guda na bakwai - Iran da Iraq da Libya da Somalia da Sudan da Syria da kuma Yemen - na barazana ga Amurka, ya ce akwai wasu 'yan Somalia a Amurka da ke da alaƙa da ƙungiyar al-Shabab.

Sai dai wani lauya da ke wakiltar jihar Washington ya faɗa wa kotun cewa dakatar da umarnin shugaban ƙasar ba zai cutar da gwamnatin Amurka da komai ba.

Babban lauya Noah Purcell ya ce haramcin ya shafi dubban mazauna jihar, inda ɗalibai ke samun jinkiri a ƙoƙarinsu na zuwa Washington, wasu kuma an hana su ziyartar iyalansu a ƙasashen waje.

An hana Musulmi shiga ko kuwa

An kwashe mintunan ƙarshe na sauraren ƙarar ana tafka muhawara a kan ko haramcin daidai yake da kulle ƙofa ga musulmai, wanda ya saɓa wa tsarin mulkin ƙasar.

Wani bayani mai shafi 15 da ma'aikatar shari'ah ta fitar a daren ranar Litinin ya yi musun cewa umarnin shugaban ƙasar bai "nuna son kai ga tsarin mutunta addini ba".

Sai dai ranar Talata a kotu, Mr Purcell ya ba da misali da jawaban Donald Trump na yaƙin neman zaɓe dangane da haramta wa musulmi shiga ƙAsar.

Ya kuma yi nuni ga jawaban da ɗaya daga cikin mashawartan shugaban ƙasar, Rudy Giuliani, wanda ya ce an buƙaci ya bijiro da wata hanya da za ta sa haramta wa musulmai shiga Amurka ya yi aiki bisa doka.

Mr Clifton ya ce haramcin ya shafi ƙasa bakwai ce kuma gwamnatin Obama da majalisar dokokin ƙasar ne suka tantance su a matsayin waɗanda suka dace a hana bai wa viza, sakamakon barazanar ta'addanci.