Ana zaɓen shugaban Somalia duk da hare-haren Al-shabab

Mogadishu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An rufe manyan titunan birnin Mogadishu da kuna hana sauka da tashin jiragen sama saboda zaben

Majalisar dokokin Somalia na zaɓar sabon shugaban ƙasar a cikin tsauraran matakan tsaro bayan ɗagawar da aka yi ta samu tsawon watanni.

Sabbin 'yan majalisun ƙasar ne ke zaɓar shugaban Somalia na gaba a cikin 'yan takara 23.

Fargabar tsaro ta sanya mayar da zabe zuwa wani killataccen wuri a filin jirgin saman Mogadishu bayan jerin munanan hare-hare daga kungiyar Al-shabab wadda ke kokarin kawo cikas a zaben.

Tun da farko an rufe manyan tituna da hana jiragen sama sauka da tashi a Mogadishu don gudanar da ɓangaren ƙarshe na zaɓen da ke da sarƙaƙiya wanda kuma aka yi ta jinkirta shi.

Ko da yake, al'ummar Somalia sun yi tarayya kan ƙabila da yare da addini, yaƙin basasa na tsawon shekaru gommai da gazawar harkokin gwamnati sun karfafa biyayya ta asalin haular da mutum ya fito, hamayya da kuma kawance tsakanin hauloli a yanzu ta mamaye rayuwar al'umma da siyasar ƙasar.

Cin hanci da rashawa, inda miliyoyin daloli ke musayar hannu sun ɓata tsarin zaɓen sai dai kokarin kungiyar Al- shabab na dakatar da shi ya gaza, duk da zafafa hare-hare da kai tashin bama-baman kunar bakin wake