An fara taro don kawo karshen yakin shekara 50 a Colombia

Bangarorin da ke yaki da juna su kan kama abokan fafatawarsu inda su kan yi garkuwa da su

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Bangarorin da ke yaki da juna su kan kama abokan fafatawarsu inda su kan yi garkuwa da su

An bude wata tattaunawar zaman lafiya mai dunbim tarihi tsakanin kungiyar 'yan tawayen Colombia ta ELN da kuma gwamnati ta hanyar wani biki a Quito babban birnin Ecuador.

Wakilan bangarorin sun yi kafada da kafada da juna a lokacin da ake buga taken kasar ta Colombia.

Babban wakilin 'yan tawaye Pablo Beltran, ya bukaci bangarorin biyu da su goyi bayan batutuwan da ke hada kansu waje daya.

Ya ce mafi rinjayen al'ummar Colombia na bukatar zaman lafiya bayan shafe sama da shekara hamsin ana tafka yaki.

A nasa bangaren, wakilin gwamnati, Juan Camilo Restrepo, ya ce ba lallai ne Colombia ta sake samun wata dama a tarihinta na wanzar da zaman lafiya ba.