Shugaba Zuma ya tura rudunar soji majalisar dokoki

Jacob Zuma

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Shugaban Afrika ta Kudu , Jacob Zuma zai ba da jawabi a kan halin da kasa take ciki ranar Alhamis

Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya bayar da umarnin a tura sojoji 440 majalisar dokokin kasar domin su tabbatar da doka da oda gabannin jawabin da zai gudanar na shekara-shekara kan halin da kasa take ciki a ranar Alhamis.

Jam'iyyun adawa sun yi Allah wadai da hakan da cewa wannan "shelar yaki ce".

A baya an sha samun zanga-zanga da fada daga 'yan adawa duk lokacin da Mista Zuma ya yi jawabi a kan halin da kasa ke ciki a majalisar dokoki, kuma 'yan majalisar dokoki na jam'iyyun adawa sun sha nuna bukatar shugaba Zuma ya yi murabus.

Fiye da shekara 10 ke nan ana zargin Mista Zuma da cin hanci da rashawa.

Ko a shekarar da ta gabata ma 'yan majalisa sun bai wa hammata iska a yayin da shugaba Zuma ke gabatar da jawabi.