'Yan sanda a Afirka ta Kuda na kashe 'yan ci rani daga Najeriya

Asalin hoton, AFP
Jami'an Nageriya na zargin 'yan sandan Afirka ta Kuda da kisa
Mai taimaka wa shugaban Najeriya a kan kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta ce an kashe 'yan kasar 116, a Afirka ta Kudu, ba bisa ka'ida ba, a cikin shekaru biyu.
A wani labari da jaridar Daily Trust ta wallafa, Abike DabiriI-Erewa, ta bayyana hakan ne bayan ganawa da Jakadan Afirka ta Kudu zuwa Najeriya, Lulu Louis Mnguni, a Abuja.
Mrs Erewa ta bayyana cewa 'yan sandan Afirka ta Kudu na kashe kusan mutane bakwai a cikin 10:
''Binciken da aka gudanar na nuna cewa a cikin shekaru biyu da suka wuce, 'yan sanda ne suka yi kashe-kashen''.
Jaridar Premium Times wadda ita ma ta wallafa labarin, ba ta bayyana lokacin da kisan mutane 116 ya faru ba.
Sai dai kuma ta bayyana damuwar Mrs DabiriI-Erewa akan yadda ake danganta 'yan ci rani daga Najeriya da aikata laifufuka a Afirka ta Kudu.
''Mun damu musamman ma game da yadda ake danganta duk wani mugun laifi a kan 'yan ci rani daga Najeriya a Afirka ta Kudu. Haka ne, wasu na aikata laifuffuka kuma ya cancanta a hukunta su amma karuwar shari'ar kisa na damun mu matuka."
Kisan dan Najeriya na baya-bayan nan a Afirka ta Kudu ya faru a watan Disambar 2016, a lokacin da 'yan sanda a birnin Cape Town suka shake Victor Nnadi har sai da ya mutu.
Mr Mnguni ya yi alkawari za a bincika kashe-kashen kuma a hukunta wadanda aka samu da laifi.