Somalia ta zabi Farmajo shugaban kasa

Asalin hoton, Reuters
An yi wa Mohamed Abdullahi Mohamed lakabi da Farmajo
Mutane na ta aikewa da sakonni a shafukansu na twitter da ke cewa karar harbi na tashi a Mogadishu, babban birnin kasar, a yayin da mutane ke murnar sakamakon zaben.
A karon farko, wani ya kawar da fargabar da mutane ke da ita ta kai ziyara kasar a shafinsa na twitter.
Mace ta farko da ta yi takarar shugaban kasa, wacce ta janye kafin takarar, ta mayar da martani a shafinta na twitter, a kan nasarar da Mohamed Abdullahi Farmajo ya yi, inda ta ce " an ceto Somalia".
Wani dan jarida a kasar ya ce mutane na ta shewa domin taya Mista Farmajo murnar nasarar da ya samu, a matsayin zababben shugaban kasar.
An dai gudanar da zaben ne a garejin jirgi da ke filin jirgi na Mogadishu, babban birnin kasar.
Somalia na fama da matsalar tsaro daga masu tsananin kishin Islama wato Al-Shabab.
Shugaba Mohamed na da shaidar zama dan kasar Somaliya da Amurka kuma ya yi suna wajen fafitukar kare hakkin bil adama.
A lokacin da yan cikin shekarun 50, ya zama firai ministan a shekarar 2011 amma ya yi murabus watanni bayan wani rashin jituwa tsakaninsa da shugaban kasar na wancan lokaci.
'Yan siyasar kasar ba su san shi ba sosai duk da yana bayyana kansa a matsayin mutumin mutane.
Mista Farmenjo ya kasance mai son shiga ajin jirgin sama na masu matsakaicin kudi, a duk lokacin da zai yi tafiya zuwa kasashen waje.
A cikin 'yan takara sama da 20, zababben shugaban ne ya fi yin fice a shafukan sada zumunta inda ake yi masa kallon dan kasa.