Ba mu yi mamakin kama jami'anmu da cin hanci ba — INEC

INEC

Asalin hoton, Channels TV

Bayanan hoto,

Wasu ƙungiyoyin 'yan Najeriya mazauna ƙasashen waje sun yi ta kiraye-kiraye a baya don a ba su damar jefa ƙuri'a

Hukumar Zabe ta Najeriya, INEC, ta ce, samun wasu jami'anta da makudan kudaden da ake zargin su da karba lokacin zaben cika gurbi a jihar Rivers, bai zo mata da mamaki ba.

Sai dai kuma hukumar, ta ce, da zarar an tabbatar da laifin da ake tuhumar su da shi, to INEC za ta dauki matakin ladabtarwa a kan jami'an nata.

Kakakin hukumar ta INEC, Nick Dazang, ya ce "Lallai idan an same su da laifin karbar hanci, to za a ba su takardar sallama daga aiki ne."

A ranar Talata ne dai wani kwamitin 'yan sanda, ya gabatar wa da Sipeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris makudan kudi da yawansu ya kai Naira Miliyan 111.

Kwamitin mai wakilcin 'yan sanda da Jami'an hukumar Farin Kaya ta SSS wanda Mataimakin Kwamishinan 'yan sanda, DCP Damian Okoro, ya ce, an sami kudaden ne daga wurin jami'an INEC guda 23.

Shugaban kwamitin DCP Damian Okoro, ya kara da cewa Naira Miliyan 111 da 300,000 wasu ne daga cikin Miliyan 360 da ake zargin jami'an hukumar sun karba, a lokacin zaben cike gurbi, a watan Disambar 2016, a jihar Rivers.

Sai dai kuma gwamnan jihar ta Rivers, Nyeson Wike ya musanta batun cewa gwamnatinsa ta bai wa jami'an INEC din na goro.