CAR: Rikici ya sake barkewa a Bangui

Asalin hoton, AFP
Dakarun da aka bincike su sun fito ne daga kasashen Burundi da Gabon
Sabon rikici ya sake barkewa a wasu sassan Bangui, babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Rahotanni sun ce akalla mutane hudu sun mutu a yankin sojojin sa-kai na PK5, ranar Talata.
Wakilin BBC ya ce, rikicin dai ya barke ne sakamakon kokarin jami'an tsaro na cafke jagoran wata kungiyar sojin kai, a inda mutunin ya yi turjiya.
Daga nan ne kuma aka fara jin tashin harbin bindiga.
Sai dai babu wasu alkaluma daga gwamnati dangane da mutanen da suka mutu kuma ba a iya tantancewa ko har da jagoran kungiyar a cikin mamatan.
Tun dai lokacin da aka hambarar da shugaba Francois Bozize a 2013, rikicin kabilanci da na addini ke barkewa da lafawa.