Shugaba Buhari na cikin koshin lafiya — Lai Mohammed

Shugaba Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An zargi gwamnatin Buhari da yin tafiyar hawainiya

Ministan yada labarai na Najeriya, Lai Mohammed, ya ce, shugaban kasar, Muhammadu Buhari yana cikin koshin lafiya.

Mista Lai wanda ya shaida wa 'yan jaridu hakan, jim kadan bayan kammala taron Majalisar Zartarwar kasar na mako-mako, ya ce, alamun lafiyar shugaba Buhari ita ce yadda ministocinsa suke aiki ba kakkautawa.

Ya yi tambaya cewa "shin kuna tunanin za mu iya gudanar da ayyukanmu su tafi dai-dai, idan da ace shugabanmu ba shi da lafiya?

Mista Lai ya kara da cewa "ba tare da nuna wani shakku ba, zan fada muku shugaba Buhari na cikin koshin lafiya."

Da man dai mukaddashin shugaban, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce lafiyar shugaban kalau har ma sun yi magana ta wayar tarho.

Batun neman karin hutu da shugaba Buhari ya yi ne dai ya janyo kace-nace a tsakanin 'yan kasar, a inda wasu ke bayyana fargabar ko shugaban ya mutu ko kuma yana fama da matsanciyar cuta.