Majalisar wakilai ta amince Burtaniya ta fita daga EU

Majalisar wakilan Birtaniya ta amince da gagarumin rinjaye kasar ta fita daga Tarayyar Turai
Bayanan hoto,

Majalisar wakilan Birtaniya ta amince da gagarumin rinjaye kasar ta fita daga Tarayyar Turai

Majalisar wakilan Burtaniya ta amince da gagarumin rinjaye ta bai wa gwamnati damar fara ficewa daga tarayyar turai, bayan kada kuri'a kan wani kudiri game da haka.

Ƙudurin dokar ya samu rinjayen 'yan majalisa 494 a kan 122, kuma a yanzu za a mika shi ga majalisar dattijan kasar.

Sakataren harkokin kasuwanci na jam'iyyar adawa Clive Lewis, na daya daga cikin 'yan jam'iyyar Labour da suka bijirewa umarninta inda suka goyi bayan ƙudurin, daga bisani kuma ya ce ya bar jam'iyyar.

A ƙarshen watan Maris ne, Fira minista Theresa May ke son fara tattaunawa a hukumance kan matakin ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai.

Za ta yi hakan ne ta hanyar bijiro da shaɗara ta 50 ta yarjejeniyar Lisbon, amma tana bukatar izinin majalisar dokokin kasar.

Shugaban jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn, ya ce ya fahimci halin tsaka mai wuya da kuri'ar ta sanya 'yan majalisar jam'iyyarsa, amma dai an ba su umarni su mara baya ga shadara ta 50 ta yarjejeniyar Lisbon, don kuwa jam'iyyar Labour ba za ta hana Burtaniya fita daga Tarayyar Turai ba.