Wasu sun kai wa 'yan sanda ƙorafi riƙe da bindiga

James Baker

Asalin hoton, FACEBOOK/JAMES BAKER

Bayanan hoto,

Jihohin Amurka sun ba da damar mallakar bindiga don kare kai

An kama wasu 'yan fafutuka kan mallakar bindiga bayan sun shiga wani ofishin 'yan sanda a jihar Michigan ta Amurka, sanye da rigar sulke da fuskar ɓad da kama kuma riƙe da wata ƙatuwar bindiga.

Mutanen waɗanda suka bayyana kansu a matsayin "masu binciken ayyukan 'yan sanda masu zaman kansu" sun ce sun je kai ƙorafi ne kuma a lokaci guda suna naɗar bidiyo kan abin da ke gudana ta Facebook.

Michigan dai jiha ce wadda mutane bisa doka na da ikon riƙe bindiga a bainar jama'a.

Sai dai 'yan sanda sun ce hatsabibancin "rashin hankali ne" da ya sanya mutane "arcewa don neman tsira".

'yan sanda sun kama James Baker ɗan shekara 24 da Brandon Vreeland mai shekara 40 nan take amma suka bayar da su beli kafin su gurfana a kotu.

James Baker ya fara ɗaukar bidiyo kai tsaye ta Facebook a wajen ofishin 'yan sandan yana cewa "Ga mu za mu shiga mu kai ƙorafi saboda tsayar da mu a gefen titi ba bisa ƙa'ida ba da 'yan sanda suka yi sa'a ɗaya da ta wuce".

"Mun ɗan ji tsoro lokacin da aka buƙaci motarmu ta tsaya a gefen hanya, don haka muka ga ya kamata mu kare kanmu," inda ya juya kyamara kan bindiga.

Sai dai suna shiga cikin ofishin, sai 'yan sanda suka zaro bindigoginsu suka ce wa mutanen su zubar da makamansu.

Kafin James Baker ya ajiye kyamarar an iya jin wani ɗan sanda cikin tsawa yana cewa "Maza, ka ajiye ta a ƙasa, ko in kashe ka. Na bindige ka!"

Sai kuma aka ji ɗaya daga cikin 'yan fafutukar na musun cewa bindigogin halartattu ne a ƙarƙashin doka.

An kama mutanen duka, kuma a cewar shafin Facebook ɗin James Baker an tuhumi kowannensu da rashin ji.