Mutumin da ke janyo taƙaddama Sessions ya zama Antoni Janar na Amurka

Jeff Sessions "na ji daɗin cikakkiyar muhawarar da muka yi"
Majalisar dattijan Amurka ta tabbatar da ɗaya daga cikin mutanen da shugaba Trump ke son naɗawa ministocinsa mafi taƙaddama, Jeff Sessions a kan muƙamin ministan shari'ah.
Ƙuri'ar ƙarshe da aka kaɗa, ta raba kan majalisa kan layin jam'iyya, inda duka 'yan jam'iyyar Dimokrat ban da mutum ɗaya suka nuna adawa da tabbatar da shi.
Matakin ya zo ne bayan jerin zaman sauraron da majalisar ta gudanar mai cike rarrabuwar kai inda ta mayar da hankali a kan tarihin ɗan majalisar dattijan na Alabama a kan batun kare haƙƙin Ɗan'adam.
An taɓa haramta wa Mr. Sessions damar zama alƙalin kotun tarayya sama da shekara 30 da ta wuce lokacin da aka zarge shi da nuna wariyar launin fata - zarge-zargen kuma da ya sha musantawa.
Yayin zaman sauraron tabbatar da shi kan muƙamin alƙali a 1986, Sessions ya taɓa kiran Ƙungiyar Kare Muradan Baƙaƙen fata ta Ƙasa a matsayin "maras kishin Amurka".