Amurka ta kashe na hannun daman Bin Laden a Syria

Asalin hoton, Getty Images
Dakarun soji sun kai harin sama na kwanaki biyu a Syria
Ma'aikatar tsaron Amurka ta bayyana cewa dakarunta sun kashe wasu mayakan al-Qaeda 11 a lokacin da suka kai musu hari ta sama a kusa da Idlib a Syria, ciki har da wani na hannun damar Osama Bin Laden.
Kakakin ma'aikatar tsaron Captain Jeff Davis, ya ce an kashe mutane 10 a harin da aka kai ranar Juma'a da ta gabata, yayin da aka kashe Abu Hani al-Masri, a harin ranar Asabar.
Rahotanni sun ce Al-Masri ne ya kafa wani sansanin horar da mayakan al-Qaeda a Afghanistan tsakanin shekarun 1980 zuwa 1990.
Yana da dangantaka mai karfi da Ayman al-Zawahiri, wanda ya zama shugaban al-Qaeda bayan dakarun Amurka sun kashe Osama Bin Laden a shekarar 2011.
Captain Davis ya ce "Wannan hari da aka kai wa al-Qaeda zai hana su shirya da kuma kai hare-hare kan Amurka da kawayenta a duniya baki daya."