Amurka: Kungiyoyin 'yan ta'adda za su dandana kudarsu

Mista Trump tare da Jeff Sessions a lokacin rantsar da shi a matsayin Alkalin Alkalan Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mista Trump ya ce lokaci ya yi da Amurkawa za su ga sauyi a shugabanci

Shugaba Trump ya sanar da matakan da gwamnatinsa za ta dauka dan rage yawan laifukan da ake yi a kasar.

Mista Trump ya yi wannan jawabi ne a lokacin rantsar da sabon alkalin alkalan Amurka, ya kara da cewa aikata laifi na karuwa a kasar dan haka gwamnatinsa za ta dauki matakin gaggawa nan ta ke.

Mista Trump ya ce lokaci ya yi da Amurkawa za su ga sauyi, a shugabancin kasar.

Mista Trump ya ce da farko zai bai wa sashen sharia da na tsaron cikin gida umarnin su dauki duk matakin da ya dace dan kawo karshen kungiyoyin masu safarar miyagun kwayoyi da suka bazu a kasar, da kuma illar da hakan ya yi ta hanyar gurbata jinin matasan Amurka.

Sabon alkalan Amurka Jeff Sessions, ya ce muggan laifukan da aka aikata a shekarar 2015 masu matukar hadari ne da ya kamata a magance su.

Mista Sessions ya ce lokaci ya yi da Amurka za ta kawo karshen kwararowar baki 'yan cirani, wanda a cewarsa ke yin barazana ga 'yan kasar wajen rasa ayyukanyi da kuma barazanar tsaron kasa.