Emirates: Kamfanin Delta Ailines ya hana mu kayan aiki

Jirgin Emirates

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Emirates ya zargi kamfanin jiragen sama na Delta Airlines da janyo masa tsaikon sauke fasinjojinsa har na sa'o'i shida

Kamfanin jiragen sama na Emirates ya sanar da cewa jirginsa da ya taso daga Seattle zuwa Dubai ya samu tsaiko na sa'o'i shida saboda kamfanin Delta Air Lines sun ki kawo mu su wani makunni da ke jikin jirgin da ya kai dala dari uku.

Babban jami'in kamfanin ya ce tun da fari an sauya abinda ake bukata a jirgin samfurin Boeing 777, amma daga bisani sai wani babban majanan kamfanin Delta ya bada umarnin a cire shi.

Kamfanin Delta dai ya kare matakin da ya dauka, ya ce wannan shi ne makunni daya da ya rage da su ke da shi a ajiye dan haka ne suka yi gaggawar ciro shi daga jirgin na Emirates saboda watakil su ma su bukace shi nan kusa.

Yawancin kamfanonin jiragen saman Amurka, sun nuna rashin amincewa da kara jiragen kasashen larabawa masu zuwa kasar da aka yi irinsu jirgin sama na Emirates.