Syria: Za mu kawo karshen gwamnatin Assad

Shugaba Assad na Syria ya sha alwashin karbe iko da sauran garuruwan da ke hannun 'yan tawaye
Sabuwar gamayyar kungiyoyin 'yan tawaye na jihadi a kasar Syria, sun ce sun yi niyyar kai mummunan hari kan dakarun gwamnatin kasar.
A watan da ya gabata ne dai aka samae da hadakar kungiyoyin mai suna Hayar Tahrir al-Sham.
Cikin kungiyoyin da suka samar da ita akwai, tsohuwar kungiyar 'yan tawaye ta al-Nusra front mai alaka da kubiyar al-Qaeda.
Kungiyoyin dai sun hade kan su ne a lokacin da aka samu baraka da rarrabuwar kawuna tsakanin wasu daga cikin 'yan tawayen.
A sakon bidiyo na farko da kungiyar ta fitar, da shugabansu Hashem al-Sheikh ya yi magana, ya ce matufar kungiyar da kuma abinda ta sanya a gaba shi ne kawo karshen gwamnatin shugaba Basharul Assad na Syria.
Shekaru biyar kenan ana yaki a kasar ta Syria, tsakanin gwamnati da 'yan tawaye, da kuma kungiyar masu tada kayar baya ta IS mai ikirarin kafa daular musulunci a kasashen Syria da Iraqi.