Niger da Amurka sun dukkufa kan tsaro

Maganar tsaro na kan gaba daga cikin abubuwan da gwamnati tasa a gabanta
Bayanan hoto,

Shugaba Mahamadou Issoufou

Kwararru ta fannin tsaro na kasashen biyu, Nijar da Amurka na gudanar da taron karfafa matakan tsaro.

Taron bitar na gudana ne a Yamai babban birnin kasar ta Nijar.

Wannan lamari dai zai tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, da ma sauren kasashen yankin Sahel masu fama da hare-haren ta'adanci.

Kasar Amurka dai na gudanar da wani shiri ne a Afirka, inda take tallafa ma kasashe 6 ta fannin tsaro.

Kasashen sun hada da Nijar da Najeriya da Kenya da Ghana da Mali da kuma Tunisiya.

To sai dai, jama'a mazauna yankunan na kokawa kan sahihancin lamarin tsaro a yankunan, ganin yadda kwalliya bata biyan kudin sabulu.

Daga nashi bangaren kakakin rundunar sojojin kasar Nijar, Kanal Mustapha Ledru, cewa ya yi kwalliya na biyan kudin sabulu,domin babu kasa a duniya, da ke da tsaro dari-bisa-dari a halin da ake ciki yanzu.