Angola: Mutane 17 sun rasu a filin wasan kwallon kafa

Taswirar kasar Angola
Bayanan hoto,

An hana magoya bayan kungiyoyin da za su buga wasan shiga fili, dalilin da ya janyo turmutsutsun kenan.

Rahotanni daga nirnin Uige na kasar Angola na cewa akalla mutane 17 ne suka rasu a turmutsutsun wani filin wasan kwallon kafa da ke birnin.

Wasu daruruwan kuma sun ji mummunan rauni, a lokacin da aka hana magoya bayan kungiyoyin kwallon kafar da ke buga wasa shiga filin.

Yawancin wadanda suka fadi kasa dai, an tattake su ya yin da wasu kuma numfashinsu ya sarke, saboda rashin ingantacciyar iska kamar yadda wani jami'in lafiya ya shaidawa BBC.

Ganau kan lamarin sun ce, mutanen da suke kokarin shiga filin wasan sun yi wa filin yawa, wanda ke daukar mutane 8,000.

Sun kara da cewa saboda yadda tutmutsutsun ya yi yawa, yawancin mutane na bi takan wadanda suka fadi kasa kafin su samu damar ficewa daga wurin.

Wasan dai kungiyar kwallon kafa ta Santa Rita de Cassia ce za ta buga da kungiyar Libolo a ranar juma'a.