Trump: Ina da wasu matakai da zan dauka kan baki

Donald Trump
Bayanan hoto,

Matakin hana wasu kasashen musulmai shiga Amurka da mista Trump ya dauka, ya janyo cece-kuce a ciki da wajen kasar

Shugaba Trump ya ce ta yiwu zai dan dakata da daukaka kara a kotun kolin Amurka na dan lokaci, kan kin amincewa da matakinsa na haramtawa wasu 'yan kasashen musulmai shiga kasar.

Mista Trump ya shaidawa manema labarai cewa, maimakon haka yanzu zai maida hankali ne kan sabbin dokokin gwamnati kan baki 'yan cirani.

Wakilin BBC yace da yake jawabi akan harsa ta zuwa birnin Florida, mista Trump ya ce ya na da matakai daban-daban da zai dauka, kuma ya na duba yiwuwar daukar wani mataki na daban kan baki 'yan ciranin, zai fara gabatar da su a farkon makon mai zuwa.

Tuni daman ya bada umarnin dakatar da bai wa 'yan kasashe 7 da musulmai suka fi yawa a ciki bisar shiga Amurka.

Tun da fari wata kotu a birnin Washington ta ki amincewa da bukatar Mista Trump ta dakatar da 'yan kasashen musulman shiga Amurkar.

Ya yin da kungiyoyin farar hula sukai ta zanga-zangar kin amincewa da matakin.

Haka kuma, kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama su ma sun ci gaba da dauko 'yan kasashe 7 zuwa Amurka.

Duk da an so hana wasu daga cikin su fita daga filin jirgin saman kasar.