Kasashe masu arzikin man fetur sun fara murmusawa

OPEC
Bayanan hoto,

Kasashen kungiyar OPEC sun yi amfani da yarjejeniyar da aka cimma ta takaita yawan mai da suke fitarwa

Farashin gangar man fetur ya daga da kashi daya da rabi a kasuwanin duniya .

Hakan ta samu ne sakamakon amincewa da kasashen kungiyar OPEC suka yi na su rage yawan man da su hakowa.

Hakan ne ya sa Hukumar kula da Makamashi ta Duniya, IEA, ta ce, kasashen kungiyar da ma wadanda ba su cikin kungiyar sun yi aiki da yarjejeniyar rage man da suka cimma.

Wannan lamari dai, ya sa kasashe masu arzikin mai sun fara murmushi,ganin hakan zai kawo sauki ga yanayin da suka samu kansu a baya.

A lokacin da farashin mai ya fadi a kasuwannin duniya, kasashe irin su Najeriya da gwamnatocin su suka dogara da kudaden shiga sun shiga mawuyacin hali.

Faduwar man kuma ta janyowa tattalin arzikin duniya girgiza, lamarin da aka dade ba a gani ba cikin shekaru masu yawa.