'Mace ba za ta iya mulkin Afirka ta Kudu ba'

Xhosa warriors

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Baraden masauratar Xhosa a Afirka ta Kudu

Wasu masarautun gargajiya a Afirka ta Kudu sun fara nuna rashin amincewarsu kan takarar shugabancin kasar da tsohuwar shugabar tarayyar Afirka Nkosazana Dlamini-Zuma ke son tsayawa.

Masarautar gargajiya ta Xhosa ta ce ba ta gamsu cewar Misis Dlamini-Zuma za ta iya jan ragamar kasar ba a matsayinta na mace.

Wani jinin masarautar Xhanti Sigcawu, wanda kani ne ga sarkin, ya ce ya yi amanna "akwai yiwuwar tana da rauni."

Ya kara da cewa, "Ganin yadda maza ma suke fama da rike shugabancin zai yi wuya mata su iya saboda yadda suke da matukar rauni."

Sarki Sigcawu ya ce ba Ms Dlamini-Zuma ba kawai, yana shakkar in akwai wata mace da za ta iya rike wannan babban mukami.

Sarkin ya yi wadannan kalamai ne a lokacin da Ms Dlamini-Zuma, wadda tsohuwar matar shugaban kasar na yanzu ce, ta kai ziyara masarautar a farkon makon nan.

Kalaman nasa sun jawo ce-ce-ku-ce sosai a kasar har ma aka rinka mayar masa da martani.

Wata fitacciyar mai sharhi kuma mai fafutuka ta rubuta masa budaddiyar wasika, inda ta ce, "Ba hurumin mai sarauta ba ne ya shiga cikin al'amarin siyasa tare da cewa ga wanda ya dace ko wanda bai dace ba."

Manyan masarautun gargajiya na Afirka ta Kudu guda bakwai ba su da karfin fada a ji a siyasa sosai, sai dai suna taka rawa wajen bayar da shawarwari.