Kungiyar Muslim Brotherhood na da alaka da Boko Haram

Nigeria

Asalin hoton, Nigerian Government

Bayanan hoto,

Ministan yada labarai na Najeriya, Lai Mohammed

Hukumomi a Najeriya sun an karar da 'yan kasar da su kula sosai da aikace-aikacen wata kungiyar mai alaka da Boko Haram, wato Muslim Brotherhood a jihar Kogi dake yakin tsakiyar kasar.

A cikin wata sanarwa, Ministan yada labarai na kasar, Alhaji Lai Mohammed ya ce kungiyar ta Muslim Brotherhood ta na shirin mallakar sinadaren hada bama-bamai, da manyan makamai domin kai hare-haren ta'addanci a wurare da suka hada da bankuna da gidajen yari da sauransu.

Ya ce bayanan sirri da aka samu sun nuna cewa cikin makaman da 'yan kungiyar ke shirin mallaka, har da bindigar harba makaman roka da ake sabawa a wuya.

Ministan ya ce bayanan sun kuma nuna 'yan kungiyar Muslim Brotherhood din suna shirin kubutar da 'yan uwansu dake tsare a Kogi da Kaduna da Abuja da karfin tsiya.

Alhaji Lai Mohammed ya kara da cewa daga cikin 'ya'yanta dake tsare da take shirin kubutar wa, har da wani mai suna Bilyaminu, wani kwararre a kungiyar.

Ministan ya yi kira ga 'yan Najeriya da su sa ido sosai sannan su kai rahoton duk take-taken da ba su gane mu su ba.