Masu zanga-zanga sun kashe dan sanda a Iraki

Iraq

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Magoya bayan Muqtada al-Sadr sun ce akwai matsalar cin hanci a Iraki

An kashe wani dan sandan Iraqi daya sannan aka raunata wasu a arangama da masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Bagadaza.

Dubban mutane ne suka fito zanga zangar, wadanda ke goyon bayan wani babban malami Muqtada al-Sadr.

Masu zanga-zangar suna fushi ne kan abin da suka kira cin hanci da rashawa da ya yi wa gwamnati katutu, sannan suna so a yi sauye-sauye a hukumar dake sa ido kan zabuka a kasar.

Arangama da jami'an tsaron ta barke ne lokacin da wasu daga cikin masu zanga-zangar suka yi yunkurin dannawa wani yanki inda gine-ginen ma'aikatun gwamnati suke.

Wasu rahotanni sun ce akwai masu zanga-zangar da dama da aka raunata.