'Shugaba Salva Kiir ne ke kitsa rikice-rikice'

south sudan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir

Rahotanni daga Sudan ta Kudu na cewa wani babban Janar na sojin kasar wanda jama'a ke girmamawa sosai, Thomas Cirillo, ya yi murabus, tare da yin kakkausar suka ga shugaban kasar Salva Kiir da makarrabansa.

A cikin wata wasika da ake ta yayatawa a tsakanin 'yan kasar, Mista Cirillo ya zargi shugaba Salva Kiir da sa kabilarshi ta Dinka ta mamaye komai a kasar.

Wasikar ta kuma zargi gwamnatin kasar da kitsa tashe-tashen hankali a Juba babban birnin kasar a watan Yulin bara, lamarin da ya lalata yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma.

Kakakin sojin kasar ya ce yana bincike game da rahotannin murabus din, amma ya ce a halin yanzu, yana daukar su a matsayin jita-jita.

Majalisar Dinkin Duniya da wasu kungiyoyi sun yi gargadin cewa akwai hadarin aikata kisan kare dangi a Sudan ta Kudun, yayin da ake ci gaba da rikici a kasar tsawon shekaru uku.