Manchester United ta lallasa Watford da ci 2-0

Manchester United Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Juan Mata mata ne ya zura kwallo ta farko kafin a tafi hutun rabin lokaci

Manchester United ta yi nasarar lallasa Watford da ci 2-0 a gasar Premier ta Ingila, abin da ya sa yanzu, maki daya ne tsakaninta da Manchester City wacce ke ta hudu a teburin gasar.

Wasanni goma sha shida kenan da Mancester United ta yi a gasar ta Premier ba tare da an doke ta ba.

Juan Mata mata ne ya zura kwallo ta farko kafin a tafi hutun rabin lokaci, sannan Martial ya zura kwallo ta biyun bayan an dawo hutun rabin lokaci.

Mai tsaron ragar Watford Heurelho Gomes ya yi kokari sosai wajen tare kwallayen da Paul Pogba da Zlatan Ibrahimovic suka so ci.

Yanzu Manchester United ta na da maki 48 a gasar, kuma maki 11 ke tsakaninta da Chelsea wacce ke sama a teburin gasar.