Koriya ta Arewa ta harba makami mai cin dogon zango

Shugaba Kin Jong-un na Koriya ta Arewa
Bayanan hoto,

Ba wannan ne karon farko da Koriya ta Arewa ke gwajin makamin kare dangi, ko mai cin dogon zango ba

Koriya ta arewa ta harba makami mai linzami da ke cin dogon zango a tekun kasar Japan.

Sojojin Koriya ta Kudu, sun ce tazarar da ke tsakanin su da inda aka harba makamin bai wuce kilomita 500 ba.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, ta tabbatar da samun raho kan gwajin makami mai linzamin da Arewa ta yi, kuma ta yi wu wannan makamin ne da ake cewa zai iya kaiwa har Amurka.

Koriya ta Arewa dai na ta gwajin makamai masu cin dogon zango a dan tsakanin nan, sai dai kuma yawanci ba ta cin nasara a gwajin na ta.

Wannan shi ne karon farko da Arewa ta yi gwajin makami mai linzami, tun shan rantsuwar kama aiki da shugaba Donald Trump ya yi, hakan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da shugaba Shinzo Abe na Japan ke ziyarar aiki a Amurkar.

Haka kuma a jiya ne Mista Trump ya yi wa Japan din alkawarin ba ta kariya, da inganta tsaron yankin.

Jami'an gwamnatin Japan sun ce, Arewa ta yi gwajin ne da gangan, dan tsokanar fada.