Brazil: Odebrecht ya bai wa kasashen Latin Amurka na goro

Odebrecht, ya yi kaurin suna wajen bada na goro dan samun kwangila
Bayanan hoto,

Zurfafa binciken da ake yi ne tun a shekarar da ta gabata, ya sa aka sake gano wasu karin mutanen da ke cikin danbarwar

Masu shigar da kara a Panama sun sanar da cewa, sun kama abokan huldar kamfanin nan da aka samu da danbarwar bayyanar wasu dubban takardun sirri na yadda manyan masu fada aji a duniya ke boye kudadensu a Panama saboda gujewa biyan haraji.

Kamen da aka yi, ya na da alaka da danbarwar cin hanci da rashawa ta miliyoyin daloli, da suka hada da kamfanin gine-gine na kasar Brazil wato Odebretch.

An dai tsare mutanen biyu Ramon Fonseca Mora da Jurgen Mossack, na kwanaki biyu dan yi musu tambayoyi, inda ake zarginsu da safarar kudaden haram.

Kamfanin Odebretch, ya tabbatar da bada na goro da suka kai Dala miliyan dari takwas, a kasashen da ke Latin Amurka.

A lokacin da aka bankado wadanda ke boye dukiya a tsibirin na Panama, Firaiministan Ingila, David Cameroon yana daga cikin su, inda ya ke fuskantar matsin lamba dangane da takardun sirrin da kamfanin lauyoyi na Mossack Fonseca ya fitar, kan safarar kuɗaɗe da kin biyan haraji.

Takardun dai sun nuna cewa kamfanin ya yi wa kamfanonin fiye da 100,000 rijista a asirce, a tsuburran da ke kusa da Birtaniya.