An lalata harsashin ginin barikin soji a Kaduna

Gwamnan Kaduna Malam Nasiru el-Rufa'i
Bayanan hoto,

Rikicin kudancin jihar Kaduna dai, ya janyo asarar rayuka da dukiya

Kudancin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya , yanki ne da jama'a suka jima suna fuskantar tashe-tashen hankulla masu halaka da addini ko kuma kabilanci.

Gwamnatin tarraya ta yanke shawarar gina barikin soji a yankin domin kai jami'an tsaro kusa da wurin.

A 'yan kwanakin baya ne babban habsan sojojin Najeriya ya je wurin domin aza harsashen gina barikin sojojin a kudancin na kaduna.

To sai dai wasu bata-gari sun lalata wannan harsashe da aka aza.Wannan lamari dai ya sa wasu 'yan kudancin jihar suka yi Allawadai game da lalata harsashin ginin Barikin Soji da aka girka.

An aza harsashin ne makwanni biyu da suka gabata domin gina barikin soji a Kafancan don kai daukin gaggawa idan wani rikici ya barke ko aka kai wani hari a Kudancin jahar.

A ganin wasu dai lalata wannan harsashin gini na barikin soji wata alama ce dake nuna adawa ga matakan da gwamnati ke dauka na samar da zaman lafiya a Kudancin na jahar Kaduna.