An sake bude cocin da Annabi Isah ya nuna mu'ujiza

tabgha Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kiristoci sun yi imanin a cocin Tabgha ne Annabi Isah, Alaihissalam ya ciyar da mutane da biredi sala biyar da kifaye biyu

An gudanar da babban taron addu'o'i don sake bude wata coci a Isra'ila, wacce Kiristoci suka yi imanin anan na Annabi Isah, Alaihissalam, ya nuna mu'ujiza da biredi da kifaye.

An lalata ginin cojin Tabgha dake kusa da koramar Galilee, lokacin da wasu yahudawa masu tsatstsaurar akida suka kai mata hari a 2015.

Shugabannin Isra'ila sun bayyana harin a matsayin laifi na nuna karan tsana.

An sake bude cocin bayan watanni takwas ana gyara ta akan kudi dala miliyan daya.

Cocin ta yi suna sosai, kuma tarihin addinin Kirista, ya nuna a nan ne Annabi Isah (AS) ya ciyar da mutane da yawa da biredi sala biyar kacal da kuma kifaye biyu.