Sudan: Hukumomi na neman wani dan ta'adda

Shugaba Omar al-Bashir na Sudan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jami'an tsaro sun bazama neman mutumin, da kuma wadanda ake zaton su na taimaka ma sa

Jami'an tsaro a Sudan sun gano sinadaran da ake amfani da su wajen hada bama-bama, da kuma fasfo bayan wani abu ya fashe a wani gida da ke babban birnin kasar Khartoum.

'Yan sanda sun ce wani mutum ya ji rauni a lokacin da ya ke kokarin hada bam, su kara da cewa ya garzaya wani asibiti da ke kusa da gidan, amma kuma sai ya tafi bayan jami'an lafiya a asibitin sun ba za su wanke masa ciwon da ke hannun shi ba sai sun shaidawa hukumomi.

A halin da ake ciki dai, jami'an tsaro sun bazama neman mutumin da masu taimaka ma sa.

Mazauna birnin Khartoum sun ce su na yawan ganin 'yan kasashen Masar, da Somalia, da 'yan Syria a gidan da abin ya fashe.

Tun dai bayan fara juyin-juya halin da ya kada a gabas ta tsakiya, da fara yakin basasar Syria, dubban 'yan kasar ke gudun hijira tare da shigowa kasar Sudan dan gujewa tashin hankali a kasar su.

Labarai masu alaka