'Yan jarida za su fuskanci hukunci a Ivory Coast

Shugaba Alasan Watara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hukumomin sun ce, idan har an samu 'yan jaridar da laifi za su fuskanci hukuncin da ya dace da abinda suka aikata

Ana saran wasu 'yan jarida shida ne za su bayyana a gaban kuliya manta sabo a kasar Ivory Coast, inda ake zarginsu da yada labaran karya.

'Yan jaridar sun yada wani labari kan cewa dubban sojojin kasar sun bijirewa gwamnati tare da bukatar a kara musu albashi a makon da ya wuce.

Mutane shidan ma'aikatan wasu gidajen jarida uku ne mallakar 'yan adawa, sun wallafa wani labari cewa gwamnatin kasar ta yi alkawarin za ta biya bijirarrun sojojin dala dubu goma sha daya kowannensu dan lallashin su sukoma bakin aiki.

Lamarin da ya sanya gwamnati ta fitar da sanarwa, kan sojojin sun bada hakuri tare da alkawarin komawa bakin aiki ba tare da an biya ko dala daya ba.

Jaridun sun wallafa cewa a yau litinin ne ake saran za a ba su kudin.