'Ya kamata MDD ta dauki mataki kan Koriya ta Arewa'

Mista Trump da Shinzo Abe
Bayanan hoto,

Mista Trump da Shinzo Abe dai, sun sha alwashin karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu

Kasashen Amurka da Japan sun bukaci kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kira taron gaggawa, domin tattauna gwajin makami mai linzami da Koriya ta Arewa ta yi a baya-bayan nan.

An dai harba makamin mai cin dogon zango a kusa da tekun kasar Japan a ranar Lahadi, kuma Koriya ta Arewar ta ce komai ya tafi yadda ake bukata.

An yi amanna da cewa makami mai linzamin zai iya daukar wasu kananan makamai masu linzami a jikinsa, yana kuma cin dogon zangon da ka iya kai wa har Amurka.

Mai bai wa shugaba Trump shawara Stephen Miller, ya sake jaddada kudurin Mista Trump na taimakawa Japan kan abinda ya kira tunzura ta da Arewa ke yi, kuma a shirye shugaba Trump ya ke ya dauki duk matakin da ya dace kan hakan.

Koriya ta Arewa dai ta ce ta yi nasara a gwajin da ta yi, kuma hakan ya jefa tsoro a cikin zukatan wasu kasashen duniya.

Fadar White House ta sanar da cewa shugaban Trump zai karfafa hadin gwiwa a yankin Pacific domin kara matsin lamba ga Koriya ta Arewar.

Masu sharhi kan al'lamuran yau da kullum sun ce sun yi imanin cewa, Koriyar ta Arewa ta shafe shekaru a baya tana bunkasa makami mai linzami da zai iya daukar goyon makamin nukiliya.