Amurka: Fargabar ambaliya ta sa dubban mutane barin muhallansu

Madatsar ruwa da ke Arewacin jihar California da ke Amurka

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Madatsar ruwan da ta fi kowacce tsawo a Amurka na cikin hadarin ambaliyar ruwa sakamakon ruwa kamar da bakin kwarya

Jami'ai sun ce katangar da aka gina domin kare ambaliyar ruwa mai tsawon mita 230 na madatsar Oroville, tana dab da rushewa.

A halin yanzu ambaliyar ruwan ya sassauta.

Sai dai, a yammacin ranar Lahadi shugaban yankin Butte, Kory Honea, ya ce har yanzu suna kan bakansu na cewa mutane su gaggauta barin gidajensu.

Yawan ruwan madatsar ya karu ne sakamakon ruwan sama mai karfin gaske da dusar kankara da aka yi bayan an kwashe shekaru da dama ana fama da fari.

Wannan ne karon farko da tafkin Oroville, wanda ke da nisan kilomita 105 a Arewacin Sacramento, ya taba fuskantar irin wannan lamarin a cikin shekaru 50 na tarihin madatsar ruwan.

A wata sanarwar da aka wallafa a shafin sada zumunta a ranar Lahadi, Mr Honea ya umurci mazauna yankin su bar muhallansu.

Ma'aikatar ruwa ta California ta yi gargadin cewa katangar da aka gina domin kare madatsar ruwa daga ambaliya wanda ke kusa da shi za ta iya rushewa.

An shaida wa mazauna garin Oroville wanda yawansu ya kai 16,000cewa su nufi Arewa.

An samu cunkoson ababen hawa a hanyar shiga cikin garin, inda wasu daga cikin mutanen da ke barin garin ke korafin cewa ya kamata a ce an yi musu gargadi tun a baya.